Wasanni

Zidane ya dauki alhakin kashin da Madrid ta sha

Kocicn Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana cewa, sun rasa jajircewa da karsashi da dagiya da rike kwallo a yayin fafatawar da suka sha kashi a hannun Real Betis, amma kocin ya amsa cewa, laifin nasa.

Mai horas da kungiyar Real Madrid Zinedine Zidane.
Mai horas da kungiyar Real Madrid Zinedine Zidane. REUTERS/Juan Medina
Talla

A cewar kocin, wannan wasan da suka yi da Real Betis shi ne mafi muni da suka gani a wannan kaka.

Kashin da Madrid ta sha ya bada mamaki, abin da ya bai wa Barcelona damar jan ragamar teburin gasar La Liga.

A makon da ya gabata ne Real Madrid ta doke Barcelona a karawar hamayya ta El-Clasico.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI