Wasanni

Ba za a sake wasa a Najeriya ba jami'an lafiya ba - ministan wasanni

Ma’aikatar wasanni a Najeriya ta bayyana shirinta na haramta duk wani wasan kwallon kafa na kwararru da babu ma’aikatan lafiya a filin wasa.

Ministan Wasanni da Matasa na Najeriya Sunday Dare
Ministan Wasanni da Matasa na Najeriya Sunday Dare Daily Trsut
Talla

Ministan wasannin kasar, Sunday Dare ne ya bayyana haka yayin ganawarsa da manema labarai a ofishinsa a Abuja, biyo bayan mutuwar wani dan wasan kungiyar kwallon kafa na Nasarawa United, Chineme Martins ana tsakar wasa a ranar Lahadi 8 ga watan Maris dinnan.

Dare ya ce daga yanzu dole ne a tanadi kayayyakin kula da lafiyar ‘yan wasa, da jami’an lafiya a filin wasa kafin ma a fara wani wasa.

Ya ce ya tattauna da masu ruwa da tsaki a harkar wasanni, kuma sun tsayar cewa daga ranar 14 ga watan Maris wannan kudiri zai fara aiki.

Ministan wasannin na Najeriya ya ce daga yanzu, an baiwa jami’an wasanni damar duba dukkanin kayayyakin kula da lafiya a filin wasa, su kuma tabbatar suna aiki, da kuma tabbatar da cewa jami’an lafiya na filin kafin ma su bari a fara wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI