Wasanni

An daga wasannin motsa jiki a Italiya saboda Coronavirus

'Yan wasan AC Milan da Juventus daaka dage karawarsu saboda annobar Coronavirus
'Yan wasan AC Milan da Juventus daaka dage karawarsu saboda annobar Coronavirus Yahoosports

An dakatar da dukkan wasannin motsa jiki na kasar Italiya har sai zuwa ranar 3 ga watan Afrilu sakamakon annobar Coronavirus, kamar yadda Firmainistan kasar Giuseppe Conte ya sanar dazu.

Talla

Wannan ya hada da gasar kwallon kafa ta Seria Aamma bai shafi kungiyoyin kasar da ke gasar Turai ba, ko kuma tawagogin wasannin kasar da ke cikin gasanni na kasa da kasa ba.

Kafin yanzu, mahukuntan gasar Serie A, babbar gasar kwallon kafa ta kasar sun ce za a buga dukkan wasannin gasar ne ba tare da ‘yan kallo ba har zuwa 3 ga watan Afrilu.

Firaminista Conte ya ci gaba da daukar tsauraran matakai na killace jama’a, ciki har da haramci kan taron jama’a a duk fadin Italiya.

Tun da farko, kwamitin shirya gasar Olympics na kasar Italiyan ne ya bada shawarar a dakatar da ilahirin wasannin motsa jiki a kasar, bayan wani taro na musamman da ta shirya na hukumomin wasannin kasar.

Italiya ce kasar Turai da wannan cuta ta coronavirus ta yi tsanani a cikinta, inda ya zuwa yanzu sama da mutane dubu 9 suka harbu, fiye da 450 kuma suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.