Wasanni-Kwallon kafa

Za mu iya haifar wa Manchester City matsala - Arteta

Mikel Arteta tare da kocinsa a Manchester City Pep Guardiola. ( Getty Images )
Mikel Arteta tare da kocinsa a Manchester City Pep Guardiola. ( Getty Images ) Getty Images

Mikel Arteta ya ce masaniyar da yake da ita game da Manchester City na iya taimakawa yayin da ya koma filin wasa na Ethihad a matsayin mai horar da ‘yan wasan Arsenal a gobe Laraba.

Talla

A watan Disamban shekarar da ta gabata ne dai Arteta, wanda ya yi aiki a matsayin mataimakin Koch Guardiola a Manchester City ya koma Arsenal.

Arteta zai ziyarci Manchester City ne da tawagarsa ta Arsenal a matsayi na 9 a teburin gasar Firimiyar Ingila, amma kuma da damar samun wuri a gasar zakarun Turai ta Europa.

Kocin na Arsenal ya ce ba shakka yana da masaniya kan irin abin da Guardiola zai yi ,ta abin da ya shafi dabaru a kokarin da ya ke na taimaka wa tawagarsa tsayawa da kafafunta bayan lallasa ta 2-0 da Manchester United ta yi a wasan hamayya.

Sai dai ya shaida wa taron manema labarai cewa ba lallai ne abin da ya sanin ya hana City yin yadda take so ba, sai dai ya san tabbas zai iya haifar mata da matsaloli.

Ya ce ranar za ta kasance mai mahimmanci a gareshi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI