Wasanni
Coronavirus ta kama dan wasan Juventus
Wallafawa ranar:
Juventus ta sanar cewa, dan wasan bayanta dan asalin kasar Italiya, Daniele Rugani na dauke da cutar Coronavirus.
Talla
Kungiyar ta ce, tana daukar matakan killace dan wasan da sauran mutanen da ya yi mu’amala da su kamar yadda doka ta tanada.
Tuni aka haramta duk wata harkar wasanni a fadin kasar Italiya saboda wannan cuta har zuwa ranar 3 ga watan Afrilu.
Mutane dubu 12 cutar ta kama a Italiya, sannan fiye da 800 sun mutu a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu