Wasanni-coronavirus

An killace 'yan wasan Real Madrid saboda coronavirus

'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid yayin murnar lashe kofi.
'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid yayin murnar lashe kofi. REUTERS/Sergio Perez

An killace ‘yan wasa da ma’aikata na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a Alhamis dinnan, yayin da aka dakatar da gasar La Liga ta kasar Spain, haka ma gasar kwallon Tennis da ta kwallon kwando, saboda annonbar coronavirus da ke tayar da hankula a duniyar wasanni.

Talla

Hukumomin La Liga sun dau matakin dakatar da manyan wasanni biyu na gasar na akalla makonni biyu, bayan da kungiyar Real Madrid din ta tabbatar da cewa ta killace babbar tawagar wasan kwallon kwandonta, sakamakon gwajin da ya tabbatar da cewa daya daga cikin ‘yan wasan tawagar ya harbu da cutar coronavirus.

Real Madrid ta ce ta yanke shawarar rufe filayen wasanninta na atisaye tare da killace ‘yan wasan, sannan ta shawarci jami’ai da suka yi aiki a filayen da su killace kan su.

Tuni dai mahukunta a gasar Serie ta Italiya suka dakatar da gasar, ganin kasar ce ta fi shan radadin wannan cuta a Turai, yayin da a Faransa aka ci gaba da gasar Ligue 1, amma ba tare da ‘yan kallo ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI