Wasanni

Magoya bayan PSG sun yi watsi da Coronavirus

PSG ta Faransa da magoya bayanta sun yi gagarumin bikin murnar doke Borussia Dortmund da ci 2-0 a karawar da suka yi a bayan fage a gasar zakarun Turai, abin da ya ba su damar samun gurbi a matakin Kwata Fainal.

'Yan wasan PSG da magoya bayansu na murnar doke Borussia Dortmund a gasar zakarun Turai
'Yan wasan PSG da magoya bayansu na murnar doke Borussia Dortmund a gasar zakarun Turai Reuters
Talla

Magoya bayan na PSG sun yi cincirindo ne a kofar shiga filin wasan na Parc de Princes da ke birnin Paris, lura da cewa, an hana ‘yan kallo shiga cikin filin saboda annubar Coronavirus a Faransa.

Sai dai jim kadan da kammala fafatawar, magoya bayan sun hade da ‘yan wasan na PSG don nuna murnarsu duk da cewa, gwamnatin Faransa ta haramta taron mutanen da adadinsu ya zarce 1,000 don hana yaduwar Coronavirus.

Magoya bayan na PSG sun yi wasan tartsatin wuta a wajen filin na Parc des Princes.

A jumulce dai, PSG ta samu nasara da kwallaye 3-2 akan Borussia Dortmund, idan aka hadada sakamakon wasansu na farko.

PSG ce ta sha kashi da ci 2-1 a gidan Dortmund a wasan zagayen farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI