Adalci shine a karkare Firimiya kafin baiwa Liverpool kofin - Shearer
Duk da cewa Liverpool ta ba da tazarar maki 25 a gasar Firimiyar Ingila a wannan kaka, tsohon dan wasan gaba na New Castle United, Alan Shearer ya yi amannar cewa ba za a yi adalci ba idan aka ayyana Liverpool a matsayin wacce ta lashe kofin.
Wallafawa ranar:
Annobar corona dai ta sa an dakatar da gasar har sai zuwa 3 ga watan Afrilu, sai dai duk da an sanya ranar dawowa, akwai rashin tabbas a lamarin kwallon kafa a nahiyar Turai.
Rashin tabbas din ne ma ya sa mataimakin shugaban New Castle Karren Brady ya bayar da shawarar cewa adalci shine, a baiwa Liverpool kofin kawai tun da ita ke kan gaba.
Duk da cewa Shearer ya ce ba ya jayayya da haka, yana ganin bai dace a ba Liverpool kofin haka kawai ba, saboda idan za a yi haka, sai dai kuma kungiyoyin da za su samu koma baya su ci gaba da zama a Firimiya, saboda ai su ma suna iya samun makin da zai hana su rikitowa.
Ya karkare da cewa, idan har gasar ba za ta kammalu ba, bai kyautu a samu wadda ya yi nasara da wanda bai yi ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu