Wasanni

Ighalo ya amince a zabtare albashinsa don zama a Manchester United

Jaridar Mail ta rawito cewa, dan wasan Manchester United kuma dan asalin Najeriya, Odion Ighalo ya amince a zabtare Pam miliyan 6 daga cikin albashinsa domin ci gaba da zaman din-din-din a kungiyar ta Manchester United.

Odion Ighalo rike da kwallo a yayin wasan Manchester United da LASK a gasar Europa
Odion Ighalo rike da kwallo a yayin wasan Manchester United da LASK a gasar Europa Reuters
Talla

Dan wasan mai shekaru 30 na zaman aro ne a Manchester United daga Shanghai Shenhua ta China har zuwa karshen wannan kaka.

Sai dai dan wasan na taka rawar gani a Old Trafford har ta kai cewa, kocinsa Ole Gunnar Solskjaer na zumudin rike shi har zuwa kaka mai zuwa.

Ighalo ya zura kwallaye hudu daga cikin wasanni takwas da ya buga wa kungiyar.

Yanzu haka, dan wasan na karbar Pam dubu 240 a kowanne mako a Shanghai, amma rahotanni sun ce, a shirye yake ya rage kashi 50 na wannan albashin domin ci gaba da zama a Manchester United.

Manchester United na da zabin sayen dan wasan bayan bude kasuwar musayar ‘yan wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI