Wasanni-Kwallon kafa

Ronaldo ba zai mayar da otel dinsa asibiti ba

Cristiano Ronaldo, dan wasan Juventus da Portugal.
Cristiano Ronaldo, dan wasan Juventus da Portugal. REUTERS/Jorge Silva/File Photo

Rahotanni daga wani otel mallakin shahararren dan wasan kwallon kafar duniya, Cristiano Ronaldo na cewa hukumomin otel din sun musanta rade radin da ake cewa za a maishe otel din asibitin wucin – gadi na kula da masu fama da cutar coronavirus.

Talla

Wata mujallar kasar Portugal, ‘MARCA’ ce ta bijiro da wannan batu, inda ta ruwaito cewa tsohon dan wasan Real Madrid din ya shirya tsaf don bayar da otel otel din sa guda biyu don taimakawa wajen yaki da cutar da ta kama sama da mutane dubu dari da 60, ta kuma kashe sama da dubu 6 a fadin duniya.

Wannan cuta dai ba ta dade da shiga kasar dan wasan kwallon kafa da ya lashe kyautar gwarzon kwallon kafar duniya ta Ballon d’Or har sau 5 ba, wato Portugal, inda adadin wadanda suka harbu ya tashi daga 76 zuwa 245.

Ma’aikata a wannan otel da ke birnin Lisbon sun ce ba su san da wani shiri da ake na maishe da otel din asibitin kula da masu dauke da cutar corona ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI