Wasanni-Kwallon kafa

Aubameyang zai nemi komawa Barcelona

Rahotanni na cewa ‘dan wasan gaba na Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang ya riga ya yanke shawarar yin hannun riga da kungiyar ta sa, kuma zai yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da haka.

Pierre-Emerick Aubameyang okaci da yake karbar kyautar gwarzon kwallon kafar Africa a 20016.
Pierre-Emerick Aubameyang okaci da yake karbar kyautar gwarzon kwallon kafar Africa a 20016. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Barcelona ce dai kungiyar da ake ganin dan wasan yake da bukatar komawa a karshen wannan kaka kamar yadda kafafen yada labarai ke ci gaba da yadawa.

Duk da cewa dan wasan gaban na Arsenal ya fito bainar jama’a yana mai bayyana kudirinsa kan kungiyar, inda yake ta nanatawa cewa yana jin dadin zama a filin Emirates, bayanan da ke zuwa kan dan wasan nan nuni da cewa Barcelona tana sanya ido a kansa, kuma tana bukatar ya dau matakin yin hannun riga da Arsenal.

Alamu na nuna cewa dan wasan ba zai iya kau da kai ba idan Barcelona ta bukaci ya taho filin wasa na Camp Nou don ci gaba da murza tamaula, duba da cewa kungiyar tasa, Arsenal tana wani matsayi ne a gasar Firimiyar Ingila wadda fafatawa a gasar zakarun nahiyar Turai ta Champions League zai yi mata wahala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI