Wasanni

An dage gasar Euro 2020 saboda Coronavirus

An dage Gasar Cin Kofin Kasashen Turai ta Euro 2020 da shekara guda, wato har nan da 2021 saboda cutar Coronavirus kamar yadda Hukumar Kwallon Kafar Turai, UEFA ta sanar.

Coronavirus ta tilasta dage Gasar Cin Kofin Kasashen Turai ta 2020.
Coronavirus ta tilasta dage Gasar Cin Kofin Kasashen Turai ta 2020. Reuters
Talla

UEFA ta dauki matakin ne a yayin wani taron gaggawa da ta gudanar ta kafar sadarwar bidiyo tare da masu ruwa da tsaki a ranar Talata.

Yanzu haka za a gudanar da gasar ta Euro 2020 daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa ranar 11 ga watan Yulin badi.

Dage wannan gasa ta Euro 2020, zai bada damar kammala manyan gasa gasa na Lig a kasashen Turai bayan an dakatar da su saboda wannan cuta.

A bangare guda, an dage gasar Copa America da aka shirya gudanarwa a Argentina da Colombia har zuwa shekara mai zuwa sakamakon Coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI