Wasanni-Kwallon kafa

'Ina koyi da Ronaldo' - Fernandes

Bruno fernandes sabon dan wasan  Manchester United.
Bruno fernandes sabon dan wasan Manchester United. Skysport.com

Dan wasan Manchester United, Bruno Fernandes ya bayyana irin dangantakar dake tsakaninsa da shahararren dan wasan kwallon kafa Cristiano Ronaldo, bayan ya bi sahun shi Ronaldon wajen komawa Manchester United daga Sporting Lisbon ta kasar Portugal.

Talla

Fernandes ya shiga Manchester United da kafar dama, inda a makonni kalilan da ya shafe a kungiyar, aka zabe shi a matsayin gwarzon dan wasa na kungiyar a wannan wata.

Dan wasan ya ce akwai dangantaka kyakyawa a tsakaninsa da Cristiano Ronaldo; suna yawan haduwa, kuma yana ba shi shawarwari masu amfani game da sana’arsa ta kwallon kafa, kuma ya yi koyi da dan wasan ne wajen komawa Manchester United daga Sporting Lisbon.

A shekarar 2003 ne Cristiano Ronaldo ya koma Manchester United daga Sporting Lisbon ta kasar Portugal, inda ya shafe tsawon shekaru 6 yana murza tamaula kafin ya koma Real Madrid a shekarar 2009.

Fernandes mai shekaru 25 abokin murza leda ne ga Cristiano Ronaldo a babbar tawagar kwallon kafar kasar Portugal, kuma sau 19 ya buga wa kasarsa tamaula tun da ya fara a 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.