Mai yiwuwa a jinkirta gasar Euro 2020
Ba mamaki a yau Talata hukumar kwallon kafa ta Turai ta jinkirta gasar cin kofin nahiyar, wato Euro 2020 da kusan shekara guda sakamakon annobar Coronavirus da ke ci gaba da tayar da hankulan al’ummar duniya.
Wallafawa ranar:
An dakatar da gaba daya manyan gasannin lig na kwallon kafa a kasashen nahiyar Turai a makon da ya gabata, a wani al’amari da ya jefa wasan kwallon kafa a cikin wani kalubalen da bai taba fuskanta ba a wannan zamani, kuma bisa ga dukkan alamu, dole ne ma a dau mataki a kan gasannin zakarun nahiyar Turai, wato Champions League da Europa League.
Hukumar kwallon kafar Turai a yau Talata za ta gudanar da wani taro ta bidiyo da wakilai 55 na hukumomin kwallon kafa na kasashe da kungiyoyi, sanna daga bisani ta gudanar da taron majalisar zartaswarta da karfe 1 agogon GMT a shelkwatarta da ke Switzerland.
A halin yanzu dai ba a san makomar gasar cin kofin nahiyar Turai, wacce dama aka shirya za ta gudana daga ranar 12 ga watan Yuni zuwa 12 ga watan Yulin wannan shekarar a birane dabam dabam na Turan ba.
Nahiyar Turai ta kasance tamkar cibiyar wannan annoba ta coronavirus, inda yanzu haka hukumomi suka garkame kofofi a Italiya da Spain, yayin da Faransa ke biye, haka kuma sauran kasashe a nahiyar suke garkame iyakoki don dakile yaduwar wannan cuta.
Fiye da mutane dubu 2 da dari 1 ne suka mutu a Italiya, kasar da za ta karbi bakoncin wasan farko na wannan gasa ta Euro 2020.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu