Wasanni
Matuidi na Juventus ya kamu da Coronavirus
Wallafawa ranar:
Dan wasan tsakiya na Juventus Blaise Matuidi ya kamu da cutar Coronavirus.
Talla
Juventus da ke buga gasar Serie A ta Italiaya ta ce, dan wasan wanda ya lashe kofin duniya tare da tawagar Faransa, ya killance kansa tun ranar 11 ga watan Maris da muke ciki.
Matuidi mai shekaru 32, shi ne dan wasan Juventus na biyu da aka tabbatar sun kamu da Coronavirus baya ga Daniele Rugani da ya kamu da ita a makon jiya.
An dakatar da daukacin wasanni a Italiya har zuwa ranar 3 ga watan Afrilu, yayin da cutar ta kashe mutane sama da dubu 2 da 500 a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu