Wasanni-Olympics-coronavirus

Babu batun dage gasar olympic ta Tokyo 2020 - IOC

Shugaban kwamitin shirya gasar Olympics na duniya ya zake cewa babu wani wa’adi na dagewa ko kuma jinkirta gasar da za a yi a birnin Tokyo a wannan shekarar, hasali ma ya ce za a gudanar da gasar kamar yadda aka tsara.

Kwamitin shirya gasar Olympics ta tabbatar da cewa gasarTokyo 2020 na nan daram.
Kwamitin shirya gasar Olympics ta tabbatar da cewa gasarTokyo 2020 na nan daram. REUTERS/Athit Perawongmetha
Talla

John Coates, wanda shine jagoran kwamitin tabbatar da wannan gasa ta Tokyo yana jawabi ne jim kadan bayan dawowarsa Australia daga Switzerland, inda yake fuskantar killacewa na tsawon makonni biyu.

Kwamitin shirya gasar ya shirya tsaf don gudanar da taron gagawa a yau Talata, yayin da ake bayyana shakkun ko zai yiwu a yi wannan gasa a yanayi na annobar coronavirus, wacce ta taka wa harkokin wasanni birki a halin da ake ciki.

A watan da ya gabata ne wani jigo a wannan kwamiti na shirya gasar Olympics, Dick Pound ya yi wani bayani mai nuni da cewa a karshen watan Mayu za a tantance ko gasar za ta gudana.

Amma Coates, wanda shine shugaban kwamitin Olympic na Australia, ya musanta batun cewa akwai wa’adi game da wannan lamari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI