Wasanni

Trabzonspor ta soke yarjejeniyarta da Mikel Obi

Tsohon dan wasan Najeriya John Obi Mikel da ya raba gari da kungiyarsa ta Trabzonspor dake kasar Turkiya.
Tsohon dan wasan Najeriya John Obi Mikel da ya raba gari da kungiyarsa ta Trabzonspor dake kasar Turkiya. AFP / Getty Images

Kungiyar Trabzonspor dake Turkiya ta soke yarjejeniyar da ta kulla da tsohon tauraron tawagar kwallon kafar Najeriya Mikel Obi, watanni 9 kacal bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar.

Talla

A watan Yunin shekarar bara ta 2019, Mikel Obi ya kulla yarjejeniya da kungiyar ta Trabzonspor ta tsawon shekaru 2.

Akwai dai yiwuwar lamarin dai ya samo asali ne bayan da Mikel ta shafinsa na Instagram, ya bukaci hukumar kwallon kafar Turkiya da ta bi sawun takwarorinta na kasashen Turai da Afrika wajen dakatar da gasar kwallon kafar kasar saboda annobar murar coronavirus.

Sai dai cikin sanarwar da kungiyar ta Trabzonspor ta fitar, ta ce bata kawo karshen yarjejeniyarta Mikel Obi ba sai da tattauna da shi kuma ya amince da hakan, amma ba ta alakanta hakan da matsayin dan wasan kan batun matakan dakile yaduwar anobar murar ta coronavirus ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI