Wasanni

Shin ya dace a mika wa Liverpool kofin firimiyar Ingila?

Ana sa ran mahukuntan gasar firimiyar Ingila su jaddada aniyarsu ta kammala kakar bana a wani taron gaggawa da za su gudanar a yau Alhamis ta wayar tarho a daidai lokacin da wasu ke cewa, ya dace a soke gasar baki daya, yayin da wasu ke ganin ya kamata a mika wa Liverpool kofin kasancewarta jagora a teburin gasar.

'Yan wasan Liverpool na yunwar kofin firimiya bayan shafe shekaru 30 ba tare da lashe kofin ba.
'Yan wasan Liverpool na yunwar kofin firimiya bayan shafe shekaru 30 ba tare da lashe kofin ba. Action Images via Reuters/John Sibley
Talla

An dakatar da dukkanin wasanni firimiya har zuwa nan da ranar 4 ga watan Afrilu saboda cutar Coronavirus.

Sai dai bisa dukkan alamu za a ci gaba da yaki da wannan cuta har gaba da watan Afrilun, abin da ya sa mahukuntan firimiyar ke shiirn sake tattaunawa don cimma wata sabuwar matsaya.

An dai dage gasar cin kofin kasashen Turai ta Euro 2020 domin bai wa manyan gasa-gasa na Turai damar kammala kakarsu nan da karshen watan Yuni.

Sai dai kungiyoyin kwallon kafar sun gaza tsayar da ranar da za su ci gaba da wasannin na lig-lig, yayin da gwamnatoci suka haramta harkokin wasanni na wucen gadi saboda yadda ake tara dubban jama’a a filayen wasannin.

To yanzu haka, watakila hukumomin lig-lig na Turai su shirya gudanar da wasanni a bayan-fage domin kammala kakar bana .

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI