FA ta tsawaita hutun dolen gasar Premier zuwa karshen Afrilu
Wallafawa ranar:
Hukumar kwallon kafar Ingila ta sanar da kara wa’adin dakatar da gasar kwallon kafar kasar a dukkanin matakai daga ranar 4 zuwa 30 ga watan Afrilu, saboda annobar murar Coronavirus da ta zamewa duniya alakakai.
An dai cimma matsayar ce bayan taron masu ruwa da tsaki kan sha’anin wasanni da kuma lafiya a karkashin hukumar kwallon kafar ta Ingila.
Har yanzu dai kungiyoyi na fatan kammala wasanninsu a dukkanin matakan gasar kwallon kafar idan aka koma filaye akan lokaci, a maimakon soke wasannin bana, ko kuma amincewa da matakin da kowace kungiya ke kai yanzu, a matsayin matakin karshe na kakar wasan ta bana.
Yanzu haka dai hukumar shirya gasar Premier Ingila ta bayyana ware dala miliyan 50, domin taimakawa kungiyoyin da tattali arzikinsu yayi kasa saboda annobar murar Coronavirus.
A farkon makon nan hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta sanar da dage gasar cin kofin kasashen nahiyar da za a yi a bana zuwa shekara mai kamawa, matakin da ake ganin zai baiwa kasashen Turan damar kammala wasanninsu na Lig, ko da kuwa bayan 30 ga watan Yuni ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu