Wasanni-Coronavirus

Fellaini ya zama dan wasa na farko Corona ta kama a Lig din China

Tsohon Dan wasan Manchester United Marouane Fellaini.
Tsohon Dan wasan Manchester United Marouane Fellaini. China Daily

Marouane Fellaini tsohon dan wasan Manchester United, ya zama dan wasa na farko a gasar kwallon kafar China ta Super League da ya kamu da cutar Coronavirus.

Talla

Cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar da Fellaini ke takawa leda Shandong Luneng, ta ce cutar ba ta kai ga kwantar da dan wasan nata ba, wanda yanzu haka aka killace.

Kamuwar Fellaini da murar Coronavirus ya dakushe fatan gasar kwallon kafar kasar ta China, na soma sabuwar kakar wasa a farkon watan Afrilu dake tafe.

A watan fabarairu aka tsara soma wasannin sabuwar kakar gasar kwallon ta China, amma barkewar annobar Coronavirus ya tilasta dage ta har zuwa abinda hali yayi, wanda samun nasarar shawo kan annobar sanya fatan komawa fili a wata mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.