Wasa ba tare da 'yan kallo ba zai rage karsashin Firimiya- Neville
Tsohon mai tsaron bayan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Gary Neville ya ce yayi wuri a dauki matakin kammala wasannin Firimiya ba tare da halartar magoya baya ba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Neville wanda ke wannan batu bayan matakin hukumomin wasanni na dakartar da ilahirin wasanni ciki har da gasar Firimiya da aka dakatar da wasanninta zuwa nan da ranar 30 ga watan Aprilu mai zuwa saboda cutar Corona, ya ce akwai matakai da tsare-tsare da ya kamata ayi amfani da su maimakon karkare wasan ba tare da halartar magoya baya ba.
Akwai dai masu ra’ayin ci gaba da wasannin na Firimiya daga ranar 30 ga watan Aprilu matukar ba a samu nasarar kammala yakar corona a Ingila ba, ta hanyar kammala gasar ba tare da baiwa magoya baya damar halartar filayen wasanni ba.
Sai dai Neville ya ce matukar hakan ya tabbata za a kammala gasar ta Firimiyar bana ba tare da armashi ba.
Kawo yanzu dai akwai hasashen da ke nuna cewa kai tsaye za a iya bayyana kungiyar da za ta iya lashe gasar ganin yadda Liverpool ke jagoranci teburi da maki 82 bayan doka wasanni 29 tazarar 25 tsakaninta da Manchester City a matsayin ta 2 kuma mai rike da kanbun.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu