Ronaldo ne a gaba da Messi a wasan kwallon kafa - Pele
Shahararren tsohon dan wasan kwallon kafa a duniya, Pele, ya tsoma baki a muhawwarar da ake na cewa wanene gwaskan wasan kwallon a tsakanin Messi da Ronaldo.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Pele ya fito karara ya ce Cristiano Ronaldo ne ke kan gaba saboda yadda a kullum harkar ba ta sabule mishi, don mafi yawancin lokuta yana samar da sakamako idan da ya shiga filin wasa.
Sai dai Pele ya ce har yanzu babu wani dan wasa da ya kai shi kansa bajinta,inda ya ce shine gwarzon gwarzaye.
Ronaldo da Messi na ci gaba da jan zarensu a harkar murza tamaula, suna kuma nuna bajinta duk da cewa shekarunsu sun ja, inda a halin yanzu Ronaldo ke wasa a Juventus ta kasar Italiya yayin da Messi ke Barcelona har yanzu.
‘Yan wasan biyu dai sun raba kyautukan gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya guda 11 a tsakaninsu, inda Messi ya lashe 6, Ronaldo 5.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu