Watakila a kai Agusta ana gasar Serie A saboda coronavirus
Shugaban hukumar kwallon kafar Italiya Gabriele Gravina ya ce zai dage wajen ganin an karkare gasar Seria A ta kasar ko da za ta kai cikin watan Agusta ne.
Wallafawa ranar:
An dakatar da dukkanin wasannin mosta jiki a Italiya har zuwa ranar 3 ga watan Afrilu sakamakon bullar cutar coronavirus, wacce ta tilasta dage gasar kwallon kafa ta Euro 2020 da ta Olympics ta Tokyo 2020.
Gravina ya ce zai yi duk mai yiwuwa don cimma burinsa, idan ma da bukatar neman goon bayan hukumar kwallon kafar Turai, EUFA da ta duniya, FIFA, ne duk zai yi hakan.
Ya ce zai zama ‘riga malam masallaci’ a fara tunanin takamammen rana, amma dole ne a yi fata na gari, ana la’akari da lafiyar ‘yan Italiya, da kuma fatan wannan annoba za ta kau nan ba da jimawa ba.
An shirya wani taro a wani lokaci a Alhamis dinnan tsakanin wakilan hukumar kwallon kafar Italiya, da na kungiyar ‘yan wasa da masu horarwa da gwamnati don yin nazari kan makomar gasar a wannan yanayi da ake ciki.
Game da batun gasar Seria A da aka dakatar, Gravina ya yi watsi da shawarar a soke ta, ko kuma a mika wa kungiyar da ke jan ragamar gasar da yawan maki kofin, inda Juventus ce a kan gaba da tazarar maki daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu