Wasanni-Kwallon kafa

Ya kamata Kane ya bar Tottenham - Alan Shearer

Dan wasan Tottenham, Harry Kane.
Dan wasan Tottenham, Harry Kane. Reuters/Paul Childs

Tsohon shahararren dan wasan kasar Ingila Alan Shearer ya ce kamata ya yi dan wasan gaba na Tottenham da ke kan ganiyarsa a Harry Kane ya bar kungiyar nan da watanni 12 idan har ba su samu lashe wani kofi ba.

Talla

Kane mai shekaru 26 yana tare da kungiyar tun a shekarar 2004 da ya shiga tawagar matasanta, kuma tun daga wannan lokaci ya zama gagarabadau amma hakan bai kai su ga lashe kofi ba sai dai ‘saura kiris’.

Dan wasan wanda yanzu haka yake kan ganiyarsa, kuma cikin shekarun da ya kamata a ce ya yagi abin da ya yaga kafin lokaci ya kure, yana ran manyan kungiyoyi, ciki har da Manchester United, wacce ake ganin a kaka mai zuwa zai koma kungiyar.

Alan Shearer dai ya shawarci Kane da ya gwada komawa wani wuri idan har zuwa karshen wannan kaka Tottenham ba ta ci wani kofi ba, to ya yi maza ya bar kungiyar.

A halin da ake ciki kwallaye 136 ne Harry Kane ya ci a gasar Firmiyar Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.