Nouri na Ajax ya farfado daga doguwar suman shekaru 3
Wallafawa ranar:
Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Ajax, Abdelhak Naouri ya farfado daga doguwar sumar da ya fada ta tsawon watanni 32 wato kusan shekaru 3 a kwance.
Naouri dan Netherland mai shekaru 22 ya fada doguwar suma ne tun bayan wata buguwa da ya yi a kaa yayin wasannin tunkarar sabuwar kaka da Ajax ta kara da Werder Bremen, a cikin watan Yulin 2017, buguwar da likitoci suka bayyana cewa ta haddasa masa tabuwar kwakwalwa ta dindindin.
A zantawar dan-uwan Nouri da gidan talabijin na Dutch a Holland, Abderrahim Nouri, ya bayyana yadda a yanzu haka dan uwan nasa ke murmurewa, ta yadda yake iya daga ido ko hannu tare da yin murmushi ko da dai har yanzu baya iya Magana ko kuma tafiya.
Acewar mahaifiyar Nouri, dan wasan tsakiar na Ajax ya nuna alamun fara magaba lokacin yana tare da abokinsa da suke taka leda a Ajax tare wato Frankie de Jong a ziyarar da ya kai masa.
Mahaifin Nouri, Mohammed Nouri, ya ce a yanzu haka sukanyi kallon kwallo ko kuma sauran wasannin talabijin tare da matashin dan nasa kuma alamu ya nuna yanajin dadin hakan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu