Wasanni

'Yan wasan Arsenal za su koma atasaye bayan zaftare musu albashi

Wasu daga cikin 'yan wasan kungiyar Arsenal.
Wasu daga cikin 'yan wasan kungiyar Arsenal. Eddie Keogh/Reuters

Kungiyar Arsenal ta ce ‘yan wasanta za su koma atasaye a mako mai kamawa, bayan daukar dogon lokaci suna hutun dole, sakamakon annobar coronavirus da ta tilastawa gwamnatocin kasashe killace miliyoyin jama’a a gidajensu don dakile yaduwar cutar.

Talla

Arsenal tace za ta koma atasayen cikin taka tsan-tsan tare da bin dokokin da kasar Birtaniya ta kafa domin yakar annobar, ciki har da kiyaye cinkoso ta hanyar rarraba ‘yan wasan nata zuwa rukuni-rukuni, wadanda za su rika motsa jiki daya bayan daya.

A makon da ya kare Arsenal ta zama kungiyar kwallon kafa ta farko a gasar Premier League, da ta cimma matsayar zaftare albashin ‘yan wasanta da masu horaswa, inda kocinta Mikel Arteta da sauran ‘yan wasa suka amince da zaftare kashi 12.5 na hakkokinsu.

Yanzu haka dai an yi wa kwallon kafa dakatarwar sai baba ta gani a Birtaniya, saboda dokar hana zirga-zirgar dake aiki don yakar annobar coronavirus, wadda kawo yanzu ta halaka sama da mutane dubu 20 a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI