Wasanni

Birtaniya ta tsaida ranar cigaba da fafata wasannin Premier

Daruruwan magoya bayan Manchester City, yayin taya 'yan wasan kungiyar da suka hada da Bernardo Silva, raheem Sterling da Kevin De Bryune murnar samun nasarar jefa kwallo a ragar abokan hamayya.
Daruruwan magoya bayan Manchester City, yayin taya 'yan wasan kungiyar da suka hada da Bernardo Silva, raheem Sterling da Kevin De Bryune murnar samun nasarar jefa kwallo a ragar abokan hamayya. Reuters

Gwamnatin Birtaniya ta bayyana 1 ga watan Yuni mai zuwa a matsayin ranar da gasar kwallon kafar Premier za ta cigaba da gudana a kasar.

Talla

Wannan albashir ga masoya kwallon kafa musamman na Ingila, ya zo ne a daidai lokacin da shugabannin kungiyoyin kwallon kafar dake gasar Premier ke tsaka da taro kan yadda za a aiwatar da sabbin tsare-tsaren cigaba da wasannin, la’akari da cewar har yanzu annobar coronavirus bata gushe ba.

Yayin sanar da matakin ta kafar talabijin, Fira Ministan Birtaniya Boris Johnson, yace gasar Premier da takwarorin da kuma sauran wasannin da ba na kwallon kafa ba, za su cigaba da gudana ne ba tare da halartar ‘yan kallo kamar yadda aka saba ba, saboda annobar coronavirus.

Yanzu haka dai kungiyoyin kwallon kafa a Birtaniya sun dukufa wajen sake tantance lafiyar ‘yan wasansu ta hanyar yi musu gwajin cutar coronavirus gami da daukar matakan kariya a filayen atasaye, motoci da masaukan ‘yan wasan a otal-otal.

A jiya Lahadi, kungiyar kwallon kafar Brighton ta sanar samun karin dan wasanta na uku da ya kamu da cutar coronavirus.

Rahotanni a baya bayan nan sun ce bayaga Ingila, wasu kungiyoyin kwallon kafa a Jamus sun bada rahoton kamuwar ‘yan wasansu da cutar ta coronavirus, a daidai lokacinda suke shirin komawa filin wasa nan da kwanaki 5 zuwa 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.