Wasanni

Sterling ya goyi bayan zanga-zangar kisan Floyd

Dan wasan Ingila mai taka leda a Manchester City, Raheem Sterling ya goyi bayan zanga-zangar adawa da wariyar launin fata a sassan Birtaniya, yana mai cewa, cutar da ake yaki da ita a yanzu, ita ce wariyar launin fata.

Raheem Sterling
Raheem Sterling AFP/Oli SCARFF
Talla

Dubban mutane suka shiga zanga-zangar mai taken “Black Lives Matter” a Birtaniya duk da gargadin da gwamnati ta yi na kaurace wa taruwar jama’a saboda barazanar cutar coronavirus.

Dan wasan ya ce, wannan wani al’amari ne mai muhimmanci a wannan lokaci, lura da cewa, tsawon shekara da shekaru kenan ana fama da matsalar ta wariyar launin.

An gudanar da gagarumin zanga-zanga a biranen London da Bristol da Manchester da Wolverhampton da Nottingham da Glasgow da Edinburgh a Birtaniya.

Kuma wannan ya biyo kisan gillar da ‘yan sanda suka yi wa bakar-fatar nan ne, George Floyd a Amurka, inda a can ma ake gudanar da irin wannan bore.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI