Hukumar FA ta dakatar da Dele Ali na Tottenham daga buga wasa 1
Wallafawa ranar:
Dan wasan tsakiya na Tottenham Dele Alli zai fuskanci haramcin wasa guda baya ga tarar Fan dubu 50 daga hukumar FA sakamakon wani bidiyonsa da ya wallafa kan coronavirus cikin watan Fabarirun da ya gabata.
Alli mai shekaru 24 dan Ingila, cikin bidiyon nasa ya nuna kansa a filin jirgin sama sanye da mayanin rufe hanci da baki sai kuma ya hasko wani dan China ta hanyar amfani da na’urar camera wajen zuko fuskarsa tukuna ya sake nuno sabulun wanke hannu, bidiyon da FA ta ce kai tsaye tsokana ce la’akari da cewa a wancan lokaci cutar ta coronavirus ta fi tsananta a China.
Sai dai tun a wancan lokaci Dele Alli ya bayyana cewa ya gano illar da bidiyon ka iya haddasawa wanda ya sanya shi gaggauta goge shi tun kafin barin filin jirgin.
Tuni dai Dele Alli ya amsa laifinsa tare da neman yafiyar jama’a kan dabi’artasa da ya ce bai kyauta ba amma yayi farin ciki da FA bata bayyana bidiyon nasa a matsayin yunkurin nuna wariya ba, ko da dai ya ce wani abokinsa ne ya zalince shi wajen yada bidiyon duk da cewa ya goge a shafinsa.
Yanzu haka dai Dele Alli zai rasa wasan da Tottenham za ta kara da Manchester United ranar 19 ga watan nan karkashin gasar Firimiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu