Wasanni-Kwallon kafa

Arsene Wenger ya bukaci rage albashin 'yan wasa

Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsenal Wenger
Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsenal Wenger Reuters/Scott Heppell

Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger ya bukaci rage albashin yan wasa domin rage radadin asarar da bangaren kwallon kafa ya fuskanta sakamakon annobar coronavirus.

Talla

Wenger ya ce daukar matakin ya zama wajibi domin ganin irin asarar da kungiyoyin suka yi wanda ya kai ga biliyoyin daloli saboda rashin wasanni da kuma cigaba da wasannin ba tare da yan kallo ba.

Tsohon manajan yace akalla wadannan kungiyoyi sun yi asarar kashi 20 na kudaden da suka saba samu daga cikin Dala biliyan 45 da suke samu a cikin shekara.

Wenger yace idan anyi nazarin albashin yan wasan dake kowacce kungiya ana iya ganewa cewar tsakanin kasha 60 zuwa 80 na kudaden da ake samu na zuwa wurin su ne, saboda haka idan an samu matsala ya dace suma suyi la’akari domin rage albashin su.

Tsohon Manajan yace rashin daukar matakin da ya dace na iya sanya kungiyoyi da dama su ruguje wanda hakan ba zai yiwa harkar wasannin fa’ida ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI