Arsenal za ta ci gaba da rike Aubameyang- Arteta

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mike Arteta.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mike Arteta. Getty Images

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mikel Arteta ya ce mataki ne mai kyau Club din ya amince da kulla sabon kwantiragi tsakaninsa da Pierre-Emerick Aubameyang wanda kwantiraginsa ke shirin karewa a watan Yunin badi.

Talla

Acewar Arteta yayin zantawarsa da manema labarai Arsenal na bukatar Aubameyang fiye da koyaushe kuma za su ci gaba da rike dan wasan don nuna masa muhimmancinsa a Club din.

Aubameyang dan kasar Gabon mai shekaru 30 tun bayan kulla kwantiraginsa da Arsenal a shekarar 2018 daga Borussia Dortmund ya zurawa Club din kwallaye 61 a wasannin 97, sai dai ya ce kawo yanzu Club din bai tuntubeshi game da batun sabunta kwantiragin nasa ba.

Akwai dai bayanan da ke nuna cewa kungiyoyin kwallon kafa na Barcelona da InterMilan su ne ‘yan gaba-gaba da ke son sayen dan wasan gaban kuma Kaftin din Arsenal matukar kwantiraginsa ya zo karshe a badi.

Arsenal da ke matsayin ta 9 a Teburin Firimiya, wasanta na farko bayan komawa daga hutun dole na coronavirus a gobe Laraba za ta yi tattaki ne zuwa Manchester City.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.