An koma fagen-daga a gasar firimiyar Ingila
Yau ake komawa gasar firimiyar Ingila bayan kwashe kwanaki 100 da dakatar da ita sakamakon annobar coronavirus, inda a yau din za a fafata tsakanin Manchester City da Arsenal.
Wallafawa ranar:
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce, har yanzu ‘yan wasansa ba su kintsa wa wannan karawar ba duk da cewa, babu wanda aka rawaitio yana fama da rauni a cikinsu.
Za a yi wasan ne ba tare da ‘yan kallo ba ko kuma magoya baya saboda matakan da aka ci gaba da aiwatar da su na hana yaduwar cutar coronavirus a Birtaniya.
Sai dai masoya kwallon kafa a sassan duniya za su samu damar kallon wasan ta kafafen talabijin.
To a bangare guda, Liverpool na fatan lashe kofin firimiyar Ingila a karon farko cikin shekaru 30, kuma muddin Manchester City ta yi rashin nasara a hannun Arsenal a , to babu shakka, Liverpool karkashin jagorancin kocinta Jurgen Kloop, za ta dage wannan kofin a ranar Lahadi da take fatar casa Everton.
Liverpool ce ke jan ragama a teburin firimiyar Ingila da banbancin maki 25.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu