Wasanni

Ni na janyo aka zazzaga wa Arsenal kwallaye- David Luiz

David Luiz na Arsenal
David Luiz na Arsenal Reuters

Dan wasan baya na Arsenal, David Luiz ya amince cewa, sakacinsa ne ya janyo har Manchester City ta zazzaga musu kwallaye a karawar da suka yi a gasar firimiyar Ingila, inda suka tashi 3-0

Talla

A karshen wannan watan ne, kwantiragin Luiz zai kare da Arsenal, amma yana fatar ci gaba da zama a kungiyar.

Dan wasan mai shekaru 33 ya ce, tawagar Arsenal ta nuna bajinta, musammam lokacin da ‘yan wasanta suka rage su 10 a kan fili, sai dai ya nanata cewa, shi ne  ya janyo musu matsala.

Luiz ne ya yi kuskuren da ya bai wa Raheem Sterling damar zura kwallon farko a ragar Arsanal, sannan kuma ya sake janyo musu bugun fanariti bayan ya riko Riyad Mahrez, abin da ya har aka ba shi katin sallama daga kan fili.

Nasarar da Manchester City ta samu ta kara jinkirta wa Liverpool burinta na lashe firimiya a ranar Lahadi da za ta hadu da Everton.

Bisa dukkan alamu Manchester City da dawo da karfinta bayan kwashe tsawon kwanaki 100 ba tare da buga gasar firimiya ba saboda annobar coronavirus.

A bangare guda, ‘yan wasan kungiyoyin biyu sun durkusa da guiwar kafarsu daya domin nuna goyon bayansu ga zanga-zangar rashin amincewa da musgunawa bakaken fata.

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce, yana jin takaici da kunya kan abin da  fararen fata ke yi wa bakaken fata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.