Leroy Sane ya ki yin hakurin zama a Manchester City
Leroy Sane na son raba gari da Manchester City kamar yadda kocinsa, Pep Guardiola ya bayyana.
Wallafawa ranar:
Manchester City ta yi ta kokarin ganin ta shawo kan dan wasan mai shekaru 24 dan asalin kasar Jamus don ganin ya ci gaba da zama a kungiyar, a daidai lokacin da kwantiraginsa ke shirin karerwa a badi.
Sai dai dan wasan wanda ake alakanta shi da komawa Bayern Munich ya yi watsi da tayin da Manchester City ta yi masa.
Guardiola ya ce, Sane na da burin komawa wata kungiya, amma a cewarsa, bai sani ba ko dan wasan zai raba gari da Manchester City cikin wannan kaka ko kuma zai hakura har kwantiraginsa ya kare a badi kafin ya tattara ina-shi-ina-shi ya bar Etihad.
A shekarar 2016, dan wasan ya koma Manchester City daga Schalke a kan farashin Euro miliyan 37.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu