Wasanni

Manchester United na fatar Pogba zai fitar da ita kunya a yau

Paul Pogba na Manchester United
Paul Pogba na Manchester United REUTERS

Kocin Manchester United, Ole Gunnar Solksjaer ya kalubalancin dan wasansa Paul Pogba da ya nuna jagoranci a yayin karawar da za su yi da Tottenham a yau Juma'a a gasar firimiyar Ingila.

Talla

Poagba wanda ya lashe kofin duniya tare da tawagar kwallon kafa ta Faransa, ya gamu da matsalar rauni a kafarsa kuma tun a cikin watan Disamba, raban da ya taka leda.

Ana sa ran dan wasan mafi tsada a Manchester United, ya nuna bajinta a yayin wannan haduwa ta anjima, inda zai tunkari tsohon manajansa, Jose Mourinho.

Solksjaer ya ce, yana da kwarin guiwar cewa, Pogba zai dawo da karsashinsa mafi kayatarwa, yayin da ya ce, yana cikin zaratan ‘yan wasan tsakiya da ake ji da su a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.