Wasanni

Liverpool na neman alfarma daga Manchester City

Tawagar Liverpool ce ta lashe kofin gasar zakarun Turai da ta gabata
Tawagar Liverpool ce ta lashe kofin gasar zakarun Turai da ta gabata REUTERS/Carl Recine

Liverpool na bukatar alfarma daga Manchester City kafin lashe kofin gasar firimiyar Ingila a karon farko cikin shekaru 30 cikin wannan mako bayan ta yi canjaras babu ci tsakaninta da Everton a karawar da suka yi a bayan-fage a ranar Lahadi.

Talla

Kiris ya rage Everton ta sauya sakamakon wasan, yayin da kwallon Tom Davies ta ci karfe, sannan kuma golan Liverpool Alisson Berker ya kade kwallon Dominic Calvert-Lewin, lamarin da ya hana Everton samun nasarar doke Liverpool a karon farko cikin shekaru 10.

Liverpool dai ta buga wasan na jiya ba tare da nuna karsashin da aka san ‘yan wasanta da shi ba.

Kodayake har yanzu kungiyar na da damar lashe gasar firmiyar ta Ingila, lura da tazarar maki 23 da ta bai wa Manchester City a teburin gasar.

Yanzu haka watakila Liverpool ta dage kofin a ranar Laraba mai zuwa a gidanta, inda za a ta fafata da Crystal Palace, amma da sharadin cewa, sai Manchester City ta yi barin maki a karawar da za ta yi da Burnley a yau Litinin.

A bangare guda kocin Liverpool Jurgen Kloop ya jinjina wa golansa, Alisson Berker bisa namijin kokarinsa wajen hana kwallaye shiga cikin ragar kungiyar a yayin wasan na jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.