Liverpool ta mika bukatar sayen Kalidou Koulbaly daga Napoli

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta mika bukatar sayen mai tsaron bayan Napoli Kalidou Koulbaly, dan wasa da ke matsayin mai tsaron baya da kungiyoyin Turai ke rububi a yanzu.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Baya ga Liverpool din kungiyoyin Firimiya ciki har da Chelsea da Man United na ‘yan sahun gaba da suka nuna bukatar sayen Koulbaly dan Senegal mai shekaru 29, ko da dai Liverpool din ce ta fara tuntubar dan wasan a hukumance.

Matukar dai Liverpool ta yi nasarar sayen dan wasan kenan Club din zai hada zaratan masu tsraon baya da ake kallonsu a matsayin mafiya karfi da rashin tsoro wato Kalidou da Virgil van Dijk dai dai lokacin da club din ke shirin lashe kofin firimiya karo na farko cikin shekaru 30.

Koulibaly wanda Napoli ta sanyawa farashin yuro miliyan 90 masu sharhi kan al’amuran wasanni na ganin abu ne mai wuya Liverpool ta iya sayen dan wasan a wannan farashi musamman ganin yadda coronavirus ta kassara bangaren kudaden shigar kungiyoyin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI