Wasanni

Sergio Ramos ya kafa sabon tarihi a La Liga

Sergio Ramos na Real Madrid
Sergio Ramos na Real Madrid Reuters

Dan wasana Real Madrid, Sergio Ramos ya kafa sabon tarihi a gasar La Liga, inda ya zama dan wasan baya mafi zura kwallaye a raga, abin da ya ba shi damar yi wa Ronald Koeman fintinkau.

Talla

Ramos ya kafa tarihin a karawar da Reaal Madrid ta doke Real Sociedad da ci 2-0 a ranar Lahadi kuma dan wasan ne ya fara zura kwallon farko a bugun fanariti a minti na 50.

Yanzu haka jumullar kwallaye 68 ya zura a tarihin gasar La Liga kuma a karo na 20 kenan a jere da yake samun nasarar jefa kwallo a bugun fanariti.

Tuni kocinsa, Zinedine Zidane ya bayyana shi a matsayin dan wasan baya mafi kwarewa a duniya.

Sai dai dan wasan ya samu rauni a yayin fafatawar ta jiya, lamarin da ya sa ya fice daga filin wasa, kuma ana ganin raunin nasa a guiwa ne, abin da ka iya zama barazana ga Madrid muddin aka tabbatar da munin raunin nasa.

A bangare guda Real Madrid ta yi kan-kan-kan da Barcelona wajen samu maki a teburin gasar ta La Liga sakamakon nasarar doke Real Sociedad.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.