Wasanni

Ranar da Liverpool za ta lashe kofin firimiyar Ingila

Liverpool na fatar dage kofin firimiyar Ingila a karon farko cikin shekaru 30
Liverpool na fatar dage kofin firimiyar Ingila a karon farko cikin shekaru 30 REUTERS/Toby Melville

Da yiwuwar Liverpool ta kawo karshen dakonta na daga kofin firimiyar Ingila a wannan makon, amma sai Manchester City ta yi barin maki a wasanta da Chelsea.

Talla

A gobe Laraba ne Liverpool za ta kece raini da Crystal Palace a Anfield bayan da ta yi canjaras babu ci tsakaninta da Everton a ranar Lahadi.

Koda kuwa Liverpool ta samu nasara a a kan Crystal Palace, ba za ta daga kofin ba har sai Manchester City ta gaza doke Chelsea a Stamford Bridge.

Manchester City na nuna bajinta tun bayan dawowa daga hutun coronavirus, inda a jiya Talata ta yi raga-raga da Burnley da kwallaye 5-0 a Etihad.

Wani abu da ya auku a yayin wannan karawa, shi ne yadda aka  ga wani jirgin sama na shawagi a sararin samaniyar filin wasan na Etihad dauke da wata shadara ta rubutu da ke cewa, "Rayukan Fararen Fata na da muhimmanci Burnley."

Magoya bayan Burnley ne suka yi shawagi da wannan jirgi, yayin da kaften din kungiyar, Ben Mee ya ce, ya ji takaicin abin da masoyan nasu suka aikata.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce, za ta zartasa da hukuncin dakatarwa ta har abada ga magoya bayan da suka aikata haka.

Wannan dai na zuwa ne bayan ‘yan wasan firimiyar Ingila sun nuna goyon bayansu ga zanga-zangar nuna bacin rai kan cin zarafin bakaken fata, inda a bayan rigunansu, aka rubuta "Rayukan Bakaken Fata na da muhimmanci."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI