Real Madrid ta dare saman teburin La Liga
Real Madrid ta dare saman teburin gasar La Liga ta Spain bayan ta samu nasarar doke Espanyol da ci daya mai ban haushi ta hannun Casemiro a karawar da suka yi a ranar Lahadi.
Wallafawa ranar:
Real Madrid ta bai wa babbar abokiyar adawarta wato Barcelona tazarar maki biyu a teburin.
Yanzu haka Madrid na bukatar lashe wasanni shida ko kuma guda biyar da canjaras daya kafin samun damar daukar kofin gasar La Liga karo na biyu tun shekarar 2012.
Atletico Madrid za ta iya yi wa Real Madrid alfarma ta hanyar kokarin doke Barcelona a haduwar da za su yi a ranar Alhamis mai zuwa a Camp Nou.
Muddin Atletico ta samu nasara akan Barcelona, hakan zai kara bai wa Real Madrid damar fadada rata tsakaninta da Barcelona.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu