Wasanni-Kwallon kafa

Barcelona ta yi cinikin Miralem Pjanic daga Juventus

Miralem Pjanic dan wasan da Barcelona ta yi cinikinsa daga Juventus.
Miralem Pjanic dan wasan da Barcelona ta yi cinikinsa daga Juventus. (Photo : Reuters)

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta kammala kulla yarjejeniyar sayen dan wasan tsakiyar Bosnia Miralem Pjanic da ke taka leda a Juventus kan yuro miliyan 60.

Talla

Barcelona ta sanar da cewa, baya ga yuro miliyan 60 a matsayin farashin dan wasan, akwai kuma karin yuro miliyan 5 da ke matsayin alawus ga Pjanic wanda kwantiragin nasa zai bashi samar shafe shekaru 4 nan gaba yana takawa Barcelonar leda.

Kungiyoyin biyu da ke tabbatar da cinikin a jiya litinin, sun ce dan wasan mai shekaru 30 zai koma Barcelonar ne da zarar an kammala wasannin wannan kaka da ya zo da tsaiko.

A bangare guda, kungiyoyin biyu na Barcelona da Juventus, sun kuma sanar da musayar Arthur Melon a Barcelonar da zai koma Juventus a wani ciniki na daban kan yuro miliyan 72 da kuma alawus din yuro miliyan 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI