Wasanni

Kocin Barcelona na fuskantar barazanar kora idan ya gaza lashe kofi a bana

Kocin Barcelona Quique Setien.
Kocin Barcelona Quique Setien. Reuters/Albert Gea

Majiyoyi da dama daga Barcelona sun tsegunta cewar hukumar gudanarwar kungiyar ta yanke shawarar korar kocinta Quique Setien muddin ya gaza lashe kofin gasar La Liga ko kuma na Zakarun Nahiyar Turai a kakar wasa ta bana.

Talla

Setien na fuskantar barazanar rasa matsyinsa ne la'akari da cewar har yanzu karsashin kungiyar na yawaitar samun nasarori bai koma kamar na shekarun baya ba, tun bayan da sabon kocin ya maye gurbin Ernesto Valverde, lamarin da ya sanya manyan jami’an Barcelona nuna rashin gamsuwa da kamun ludayin Setien.

Rahotanni sun ce ko a baya bayan nan an samu rikici tsakanin kocin na Bercelona da wasu ‘yan wasansa, jim kadan bayan wasan da suka tashi 2-2 tsakaninsu da Celta Vigo ranar Asabar a gasar La Liga, abinda ya baiwa abokiyar hamayyarsu Real Madrid damar darewa saman tebur da tazarar maki 2.

A yau talata kuma Barcelona za ta sake fuskantar wani sabon kalubalen, domin kuwa za su fafata ne da daya babbar abokiyar hamayyarta Atletico Madrid a gida, wato filin wasa na Camp Nou.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI