Bakonmu a Yau

Tattaunawar Victor Osimhen da Antwan Gro-nyee bayan lashe kyautar zakaran Ligue 1 a Faransa

Wallafawa ranar:

Dan wasan gaba na Najeriya da ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Lille da ke Faransa Victor Osimhen ya lashe kyautar dan wasan da ya fito daga Afirka wanda yafi fice a gasar League 1 da ake bayarwa kowacce shekara, wanda tashar RFI ta sanya sunan tsohon dan wasan Kamaru Marc Vivien Foe.

Dan wasan Najeriya Victor Osimhen da ke taka leda a Lille ta Faransa.
Dan wasan Najeriya Victor Osimhen da ke taka leda a Lille ta Faransa. AFP
Talla

A wannan shekara dan wasan Algeria Islam Slimani da ke yiwa Monaco wasa ya zo na 2, yayin da Yunis Abdelhamid na Stade Rennais ya zo na 3.

'Yan jaridu marubutan labarin wasanni a Faransar ne suka tantance 'yan wasa 11 da suka shiga takarar lashe kyautar, yayinda suka zabi Osimhen.

Osimhen wanda ya koma Lille bara domin maye gurbin Nicolas Pepe da ya koma Arsenal, ya jefa kwallaye 13 da kuma taimakawa a jefa wasu 4 a wasanni 27 da ya bugawa kungiyar.

Bayan RFI ta mika masa kyautar, Antwan Gro-nyee ya tattuna da shi, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi