Wasanni-Kwallon kafa

Zan so na dauki tsawon lokaci ina taka leda a Liverpool- Salah

Dan wasan gaba na Liverpool zakarar Firimiyar Ingila, Mohamed Salah ya ce yana fatar daukar tsawon lokaci ya na taka leda ga Club din.

Dan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah.
Dan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah. GEOFF CADDICK / AFP
Talla

Salah dan Masar mai shekaru 28 da ke matsayin dan wasa mafi zura kwallaye cikin wannan kaka a Club din, yayin zantawarsa da jaridar wasanni ta BeIN ya ce yana da yakinin Club din ya jima yana jan zarensa wajen lashe kofunan gasar Turai daban-daban.

Mo Salah wanda Liverpool ta sayo daga Roma a 2017 ya taka rawar gani a nasarorin Club din na dage kofin zakarun Turai kakar da ta gabata, da kofin zakarun duniya ajin kungiyoyi a bana da kuma kofin Firimiya da suka dage makon jiya karon farko a shekaru 30.

A cewar Salah ya na matukar kaunar Liverpool kuma yana jin dadin doka wasanninsa karkashin Club din dalilin da ya sanya shi fatan daukar tsawon lokaci yana taka leda.

Ya zuwa yanzu dai kwallaye 92 Salah ya zurawa Liverpool a wasanni 145 tun bayan kulla kwantiraginsa da Club din ciki kuwa har da 21 da ya zura a wasanni 41 cikin wannan kaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI