Gasar Premier: West Ham ta doke Chelsea, Arsenal ta lallasa Norwich
A cigaba da fafata gasar Premier dake kasar Ingila, West Ham ta haifar da cikas ga burin Chelsea na kammala gasar ta bana a tsakanin kungiyoyi hudu na farko.
Wallafawa ranar:
Yayin wasan na jiya da suka fafata dai West Ham ta doke Chelsea ne da kwallaye 3-2, abinda ya sa a har yanzu kungiyar ta Chelsea ke mataki na 4 a tebur da maki 54, maki 2 kacal tsakaninta da Manchester United wadda a baya ta baiwa rata mai yawa.
A nata bangaren kuwa Arsenal lallasa kungiyar Norwich ta yi da kwallaye 4-0.
Wannan nasara dai ta baiwa Arsenal damar komawa matakin ta 7 da maki 46, cike da fatan samun gurbi ko dai a gasar Europa ko kuma ta zakarun turai.
A sauran wasannin da aka fafata AFC Bournemouth ta sha kashi a hannun Newcastle United da 4-1, sai kuma Everton da ta doke Leicester City da 2-1.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu