Wasanni

Manchester City na da kwarin gwiwar kotu ta sauya hukuncin UEFA- Guardiola

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola ya ce yana da kwarin gwiwar hukumar UEFA za ta sauya hukuncin da ta zartas kan Club din na dakatarwa shekaru 2 saboda karya ka’idojin sayen ‘yan wasa.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola Reuters/Daniel Kramer
Talla

A watan da ya gabata ne City ta daukaka kara kan hukuncin na UEFA zuwa kotun sauraren karakin wasanni, kuma a ranar 13 ga watan nan ne ake saran a fara zaman saurarn karar, wanda Club din ke da kwarin gwiwar zai yi nasara.

A cikin watan Fabarairun da ya gabata ne, hukumar UEFA ta yankewa Manchester City hukuncin dakatarwar shekaru 2 da biyan tarar yuro miliyan 30 sakamakon karya kaidoji wajen zuba kudin da ya wuce kima a sayen ‘yan wasa baya ga kin bayar da hadin kai yayin binciken da hukumar ta kaddamar kan Club din.

Sai dai a zantawar Guardiola da manema labarai, ya ce suna da yakinin hukuncin zai suya, wajen basu damar shiga a dama dasu a gasar cin kofin zkarun Turai da bai taba zuwa Club din ba.

Matukar dai hukuncin na UEFA bai sauya ba, kenan City ba ta da hurumin taka leda karkashin dukkannin manyan gasar Turai, yayinda rashin shiga gasar zakarun Turai zai sanya Club din asarar fiye da dala miliyan 127.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI