Wasanni-Kwallon kafa

Kamfanin Pirelli za ta taimaka wa Inter dauko Messi

Shugaban kamfanin kera tayoyi na Pirelli Marco Tronchetti ya ce kamfanin wanda ke daukar nauyin rigar ‘yan wasan Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan zai iya taimkawa wajen ganin Inter ta sayi dan wasan Barcelona Lionel Messi, sai dai ya ce dole ne shugaban kungiyar kwallon kafar, Steven Zhang ya yi wani yunkuri a bangarensa.

Dan wasan Barcelona Lionel Messi
Dan wasan Barcelona Lionel Messi REUTERS/Waleed Ali
Talla

A wannan karon ma kafafen yada labarai na tsokaci a game da makomar Messi a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, inda ake cewa zai bar kungiyar da zarar kwantiraginsa ya kare a shekarar 2021.

A baya can an sha alakanta Lionel Messi da canza sheka zuwa kungiyar Inter ta Italiya, inda shugaban kungiyar na lokacin Masimo Moratti ke cewa babu aibi idan dan wasan wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasa na duniya har sau 6 ya koma kungiyar.

Sai dai Tronchetti ya yi kashedin cewa matsalar annobar coronavirus zai iya kawo tarnaki kan yadda kamfanin zai taimaka kamar yadda kamfanin kera motocin Fiat ya yi wa Juventus wajen sayen Cristiano Ronaldo a 2018.

Messi wanda ya ci kwallaye 22 ya kuma taimaka aka ci 19 a gasar Laligar wannan kaka bai ce uffan ba a game da wannan batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI