Mourinho ya lashe wasanni 200 a Firimiya
Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta Ingila, Jose Mourinho ya samu nasara ta dari 2 a gasar Firimiyar Ingila bayan tawagarsa ta doke Everton a daren Litinin.
Wallafawa ranar:
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne dai wasa tsakanin kungiyoyin biyu ya dauki wani salo mara dadi, musamman ma ga Totenham, amma sauki ya samu, sakamakon kwallo daya da Tottenham ta samu ta wajen cin gida da dan wasan Everton Michael Keane ya yi.
Wannan nasarar ta karfafa wa Tottenham gwiwa a kokarin da take na ganin ta kasance a jerin kungiyoyi 6 na farko a teburin gasar Firimiya, don a dama da ita a gasar Europa ta badi.
Mourinho ya samu cikas ta wajen samun nasara a wasanni tun da ya kama aiki a Tottenham a watan Nuwamba, amma ya kafa tarihi mai mahimmanci a karawarsa da Everton.
Kocin ne mai horarwa na 5 da ya cimma wannan matsayi na nasarori 200 a gasar firimiya bayan Alex Ferguson, Arsene Wenger, Harry Redknapp da David Moyes.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu