Osimhen na iya kulla yarjejeniya da Napoli
Dan wasan gaban Lille, kuma dan Najeriya, Victor Osimhen ya shirya don yanke shawarar komawa kungiyar kwallon kafa ta Napoli bayan ganawar da ta gudana tsakaninsa da kocin kungiyar Gennaro Gattuso da shugaban kungiyar Aurelio De Laurentiis, a cewar wakilinsa Osita Okolo.
Wallafawa ranar:
Ana ta alakanta dan wasan da komawa gasar Serie A, bayan bajintar da ya nuna a gasar League 1 ta Faransa lamarin d ya kai shi ga samun kyautar gwarzon dan wasa a shekarar da ta gabata a Faransan.
A makon da ya gabata Osimhen ya ziyarci Italiya don ganawa da shugabannin kungiyar Napoli kan kwantiragin da suke mai tayi, sai dai wakilinsa ya ce dan wasan ne kawai ke da hurumin yanke hukuncin karshe a game da canza shekar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu