Wasanni

Abraham na son Chelsea ta rubanya masa albashi

Dan wasan Chelsea Tammy Abraham ya shaida wa kungiyar cewa, yana son babbar yarjejeniyar da za ta sa ya rika kwasar albashin Pam dubu 130 a kowanne mako.

Tammy Abraham
Tammy Abraham vanguardngr
Talla

Jaridar Times ta rawaito cewa, dan wasan na zumudin a rika biyan sa kwatankwacin albashin da takwaransa Callum Hudson-Odoi ke karba, lura da cewa, tare suka kammala wata makarantar horar da ‘yan wasa.

Yanzu haka, Abraham na karbar Pam dubu 50 ne a mako karkashin yarjejeniyar da za ta ci gaba da zaunar da shi a kungiyar ta Chelsea har zuwa shekarar 2022.

Abraham na nuna bajinta tun bayan komawarsa Stamford Bridge, inda ya jefa kwallaye 15 a raga a wasannin da ya buga wa kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI